in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafa kungiyar sada zumunci tsakanin Sin da Masar a Alkahira
2018-05-14 10:06:55 cri

Jiya Lahadi 13 ga wata, an yi bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafa kungiyar sada zumunci tsakanin Sin da Masar a birnin Alkahira. Jakadan Sin dake Masar Song Aiguo, mataimakin shugabar kungiyar sada zumunci tsakanin Sin da kasashen waje Madam Lin Yi, da mataimakin shugaban kungiyar sada zumunci tsakanin Sin da Masar Ahmed Wally da dai sauran manyan jami'ai sun halarci bikin.

Ahmed Wally ya ce, Masar da Sin na kai ga matsaya daya kan wasu batutuwan kasashen duniya, kuma zaman lafiya da bunkasuwa, babban buri ne na kasashen biyu baki daya, abin da ya samar da tushe mai inganci wajen kara hadin kai tsakanin kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu, kasashen biyu na hada kai a wasu manyan ayyuka, ciki hadda yankin raya tattalin arziki dake arewa maso yammacin Gulf Suez, tasoshin jiragen ruwa, na'urorin wutar lantarki, layin dogo, gine-gine da dai sauransu, ayyuka dai dake shaida hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

A nata bangare kuma, Madam Lin Yi ta ba da jawabi cewa, Masar ta kasance kasa ta farko a yankin Afrika da Labarawa dake kafa dangantakar diplomasiyya da kasar Sin, zumuncin dake tsakaninsu na da inganci sosai. Sin kuma na dora babban muhimmanci kan hadin kai da Masar, a shekarun da suka gabata, dangantakar tsakaninsu na samun bunkasuwa yadda ya kamata. Ta ce, zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu tushe mai inganci ne ga dangantakar gwamnatocin biyu, ana bukatar bangarori daban-daban da su kara sada zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China