A halin yanzu, rundunar sojojin dimokuradiyya mai adawa da gwamnati dake karkashin jagorancin dakarun Kurdawan, ta mamaye galibin yankunan dake arewa da kuma gabashin kasar.
Bisa labarin da aka samu, an ce, tawagar wakilan kwamitin dimokuradiyyar Syria ta yi shawarwari da wakilan gwamnatin kasar a ranar 26 ga wata, inda a fili ne suka tattauna batun yankunan da dakarun Kurdawan suka mamaye a arewa da kuma gabashin kasar karo na farko.
Sa'an nan, kwamitin dimokuradiyyar ya sanar a ranar 28 ga wata cewa, shi da gwamnatin kasar sun cimma matsaya guda, kan kafa wata kasa mai bin salon dimokuradiyya, da aka rarraba ikonta tsakanin sassa.
Bugu da kari, an fidda rahoto cewa, sojojin gwamnatin kasar Syria sun sami ci gaba kan aikin yaki da kungiyar IS a yankin Yarmuk dake kudancin kasar. Kuma, an ce, bi da bi sojojin gwamnati sun kwato garuruwa guda 8 dake yankin Yarmuk, bayan suka kai hari a yankin dake karkashin ikon kungiyar IS dake yammacin lardin Daraa na kasar. Sai dai kuma ya zuwa yanzu, akwai sauran garuruwa da kauyuka guda 6 dake kudu maso yammacin kasar Syria wadanda ba a kwato su ba. (Maryam)