in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD ya gudanar da taron tuntuba a kokarin warware rikicin Syria
2018-06-26 10:51:17 cri

Manzon musamman na MDD game da batun Syria Staffan de Mistura, ya gudanar da wani taron tuntuba jiya Litinin a Geneva, da wakilan kasashen Faransa da Jamus da Jordan da Saudiyya da Birtaniya da Amurka, game da tattaunawar da MDD ke shiryawa domin warware batun Syria a siyasance.

Cikin wata sanarwar da aka fitar a jiyan, Staffan de Mistura ya ce yayin taron, an yi musayar ra'ayoyi da karin bayanai game da yanayin da ake ciki yanzu.

Sanarwar ta ruwaito jami'in na cewa, an kuma bayyana damuwa ainun game da ta'azzara ayyukan soji a kudu maso yammacin Syria, tare da yin kira da a kawo karshen rikicin nan take.

Tattaunawar MDD ta karshe da aka yi kan rikicin Syria ta kare ne a watan Disamban bara a Geneva, inda Staffan de Mistura ya bayyana ta a matsayin 'asarar wata babbar dama'. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China