in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Syria sun harbo jirgin yakin Isra'ila
2018-07-09 09:44:17 cri
Rahotanni daga kasar Syria na cewa, sun harbo wani jirgin yakin Isra'ila a lokacin da jiragen saman yakin Syria ke kai hari ta sama a kan sansaninsu na T-4 dake tsakiyar kasar a jiya Lahadi.

Wata sanarwa da sojojin kasar suka bayyana da kafar talabijin ta ce, makaman da sojojin suka harba ta sama sun tilastawa wasu jiragen yakin Isra'ilan barin sararin samaniyar kasar ta Syria, bayan da wani makami ya fada kan wani jirgin yaki, kana sun yi nasarar dakile wasu makamai masu linzami da aka harbo.

Sai dai rahoton bai yi wani karin haske game da jirin yakin Isra'ilan da aka samu ba. Wannan ba shi ne karon farko da sojojin na Syria ke harba makamai kan jiragen yakin Isra'ila ba. Koda a watan Fabrairu sojojin na Syria sun harbo wani jirgin yakin Isra'ila samfurin F-16 a arewacin Syria。

A halin da ake ciki, gidan talabijin na Syria ya ce, makamai masu linzami guda 6 sun fada harabar sansanin sojojin yayin kai harin na ranar Lahadi,inda suka haddasa barna, sai dai har zuwa wannan lokaci babu rahoton jikkata ko asarar rayuka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China