Xie Xiaoyan ya ce, a yayin ziyarar tasa a kasar Syria ta wannan karo, kasashen Sin da Syria, sun cimma matsayi daya kan harkokin inganta yunkurin siyasa, da yaki da ta'addanci, da kula da 'yan gudun hijira, da kuma halartar aikin sake gina kasar ta Syria.
Ya ce kasar Syria ita ma tana fatan Sin za ta ba da taimako, kan ayyukan warware matsalar kasar ta hanyar siyasa, musamman ma kan harkokin kula da 'yan gudun hijira, da kuma sake gina kasar da dai sauransu. (Maryam)