ICRC ta fada cikin wata sanarwa cewa, dubun dubatar mutane a yankin na Daraa suna cikin garari, a yayin da ake gwabza yaki tsakanin sojojin Syria da kungiyoyin 'yan tawayen kasar a yankunan dake karkashin ikon 'yan tawayen a sassan lardunan kasar da suka hada da Quneitra da Sweida.
Kungiyar ta Red Cross ta bukaci bangarorin dake yaki da juna dasu nuna tausayi domin kaucewa salwantar rayukan fararen hula.
Da take bada tabbaci game da samar da tallafin jin kai ga wadanda tashin hankalin ya daidaita, ICRC tace, fararen hula suna da 'yancin tserewa tashin hankalin don neman mafaka da kuma kariya.