in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana damuwa game da tsaron fararen hula a kudancin Syria
2018-07-19 09:54:42 cri
MDD ta bayyana damuwa matuka, game da tsaron fareren hula da rikici ya rutsa da su a kudancin Syria, biyo bayan ci gaba da daukar matakan soji a yankunan Daraa da Quneitra.

Kakakin MDD Farhan Haq, ya ce Rahotanni na cewa, luguden wuta da ake ci gaba da kai wa garin Nawa dake yammacin Daraa na sanadin karuwar asarar rayuka da jikkatar mutane, baya ga hana asibitin wucin kwaya daya tilo na garin, wanda ke kula da wadanda suka jikkata gudanar da aiki.

Farhan Haq, ya kara da cewa, MDD na ci gaba da kira ga dukkan bangarori a kasar su tabbatar da kare fararen hula da matsugunansu, kamar yadda dokar jin kai ta kasa da kasa ta tanada.

Ya ce MDD ta kuma yi kira da a tabbatar da samun dorewar damar kai agaji ga masu bukata cikin aminci ba tare da wani cikas ba, ta hanyoyin da za su isa gare su kai tsaye.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasashen Larabawa dake Syria, ta kai kayakin agaji na MDD ga mutane kusan 10,000 a yankuna 6 na gabashin Daraa, wanda ya koma karkashin ikon gwamnatain kasar a baya-bayan nan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China