in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Syria sun sake kwace yankunan dake kusa da iyakar Iraki daga hannun IS
2018-06-25 09:56:36 cri
Rundunar sojan Syria ta ce dakarunta sun yi nasarar sake kwace yankunan da suka kai murabba'in KM 1,800 a gabashin Syriar kusa da kan iyakar kasar Iraki daga hannun mayakan IS.

Wata sanarwa da rudunar sojan kasar Syria ta fitar, ta ce dakarun kasar da kawayenta sun kai wasu hare-hare kan wasu yankuna dake hannun mayakan IS a lardin Deir al-Zour dake gabashin kasar, inda suka yi nasarar kwato yankunan dake wajen Deir al Zour yamma da birnin al Bukamal a kusa da kan iyakar kasar Iraki.

Wannan dai wani bangare ne na matakan sojan da sojojin Syriar ke dauka a yankin hamadar gabashin kasar, inda a 'yan kwanakin nan sojojin suka yi nasarar sake kwace yankuna masu tarin yawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China