Jagoran masu binciken Zayeur Khan, ya ce suna fatan amfani da wani tsari na musamman a binciken da zai gudana a cibiyar ta ICIPE, kan wata nau'in ciyawa dake dakile yaduwar wannan tsutsa cikin sauri. Ya ce ana bukatar samar da wata fasaha mai araha, da rashin illa ga muhalli, wadda mai yiwuwa ta kunshi gauraya nau'o'in tsirrai daban daban a gona guda, ciki hadda wadanda ke dakile yaduwar wannan tsutsa, a matsayin wata dabara ta kawar da barazanar tsutsar.
Mr. Khan ya kara da cewa, suna fatan bincikensu zai magance kalubale 5 da ake fuskanta a gonaki; abubuwan da suka kunshi matsalar hada kiwo da noman amfanin gona, da dakile yaduwar kwari, ko ciyayi, da ma matsalar zagwanyewar albarkatun kasa da danshin ta.
Tsutsar FAW ta kasance babban kalubale ga manoma, don haka ya zama wajibi a dukufa wajen gano fasahohin magance ta, kamar dai yadda Khan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan. (Saminu Hassan)