in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Kenya da ta kawar da gibin dake tsakanin jinsi a bangaren bada horon sana'o'i
2018-06-24 15:21:38 cri
MDD ta bukaci kasar Kenya da ta kawar da gibin dake tsakanin maza da mata a bangaren bada horo kan sana'o'in dogaro da kai domin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar.

Karin Fueg, mataimakiyar daraktar kula da al'amurran mata ta MDD a Kenya, ta bayyana a Nairobi cewa, mata kalilan ne suke aikin a bangarori masu muhimmanci kamar bangarorin masana'antu, samar da gidaje da gine gine wadanda galibi maza ne suka mamaye bangarorin.

"Babu wata hanya mafi sauki wajen kawar da gibin da ake da shi a fannin bada horo kan sana'o'i illa a hada karfi da karfe tsakanin bangaren gwamnati, da cibiyoyin bada horo da su kansu matan wajen shiga a dama da su domin su ci moriyar irin damammakin da ake da su a halin yanzu," Fueg ta fadi hakan ne a lokacin bikin ranar da aka kebe ga matan da mazajensu suka rasu ta kasa da kasa.

Fueg ta ce, mafi yawan shirye shiryen bada horo da ake da su a halin yanzu da shirin samar da sana'o'i da ake ci gaba da bullo da su an fi danganta mata da sana'o'in dinki, gyaran gashi, da kuma saka.

Ta bukaci gwamnati da ta kara zuba jari a wannan bangare, kana bangarori masu zaman kansu da kungiyoyin bada tallafi su taimaka wajen shawo kan gibin da ake samu tsakanin jinsi a bangaren bada horo kan sana'o'i ga mata marasa galihu wajen samar musu damammakin samun horo da kuma ba su kayan aiki ga matan musamman matan dake zaune a yankunan karkara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China