in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zartas da sanarwar Nairobi a gun taron neman samun bunkasuwa a fannin cinikayya na MDD
2016-07-23 12:42:52 cri

An rufe taron neman samun bunkasuwa a fannin cinikayya na MDD karo na 14 a jiya Jumma'a a birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya, inda aka zartas da sanarwar Nairobi wadda ta bayyana sakamakon da aka samu a gun wannan taro.

Sanarwar ta ce, a matsayin muhimmiyar hukuma ta MDD, taron neman samun bunkasuwa a fannin cinikayya na taka muhimmiyar rawa wajen daidaita batutuwan kudade da fasahohi da zuba jari da kuma neman samun bunkasuwa mai dorewa a duniya.

Sakataren taron Mukhisa Kituyi ya bayyana cewa, bisa sanarwar Nairobi, kasashen duniya za su ci gaba da kokarin neman samun bunkasuwa mai dorewa a duniya, tare da habaka cinikayya a tsakanin kasa da kasa da kuma ba da taimako ga jama'ar kasashe masu tasowa.

Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Kenya wanda ya halarci bikin rufe taron ya yi jawabi,ya ce sanarwar Nairobi ta bayyana matsaya guda da aka cimma a gun taron za ta taimaka wajen gaggauta yunkurin tabbatar da zaman wadata a duniya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China