Sakataren ma'aikatar masana'antu ta kasar Adan Mohamed, ya shaidawa wani taro kan cinikayya jiya a Nairobi cewa, kasar ta shirya abubuwan da za su ja hankalin masu zuba jari da suka hada da matakan haraji da raya ababen more rayuwa, don zamar da kasar wuri mafi arhar sarrafa kayayyaki.
Ya ce suna son masu masana'antu na kasar Sin, su taimkawa Kenya cimma burinta na zama jagora a fannin fitar da kayayyaki zuwa sauran sassan duniya.
Adan Mohamed, ya ce masu masana'antun na kasar Sin za su iya cin gajiyar arhar kudin kwadago domin samar da kayayyaki a cikin kasar da ma kasuwannin kasashen waje.
Ya ce kasar ta riga ta kaddamar da yankin raya tattalin arzikin na farko, wanda ya samar wa masu zuba jari ababen more rayuwa masu inganci irin na sauran kasashen duniya, domin su samar da hajojin da za su yi takara a kasuwanni duniya.
Har ila yau, ya ce an yarjewa masu zuba jari fitar da ribarsu zuwa kasashensu ba tare da wani tarnaki ba. (Fa'iza Mustapha)