Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya bayyana kaduwa da labarin rashin samun wanda ya tsira daga hatsarin da ya rutsa da wani karamin jirgin sama a yankin tsakiyar kasar.
Shugaba Kenyatta ya ce, ya yi bakin ciki matuka, kuma gwamnatinsa za ta ba da taimako da ake bukata ga iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su.
Sanarwar da ya fitar ta kuma tabbatar da cewa, za a tabbatar da gudanar da bincike don fahimtar musababbin hatsarin.
Babu wanda ya tsira daga cikin mutane 10 dake cikin jirgin da ya fadi a saman jerin tsaunukan Aberdare. (Fa'iza Mustapha)