A yayin taron, Yang Jiechi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen BRICS su karfafa hadin gwiwarsu a fannonin kiyaye zaman lafiya da inganta ci gaba da kuma harkokin kasa da kasa yadda ya kamata, domin ba da gudummawa ta fuskar tsaro da zaman karko a duniya.
Ya kuma jaddada cewa, ganawar da shugabannin kasashen BRICS suka yi a birnin Xiamen na kasar Sin a bara, ta bude wani sabon shafin hadin gwiwar kasashen cikin shekaru 10 masu zuwa. Ya ce ya kamata a aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen suka cimma da kare ka'idojin MDD da tsayawa tsayin daka wajen warware sabanin dake tsakanin kasa da kasa a siyasance da karfafa hadin gwiwa a fannin kare tsarin siyasa da moriyar kasashe masu tasowa da kasashe masu samun saurin ci gaban tattalin arziki, ta yadda za a gina sabuwar dangantaka tsakanin kasa da kasa da kuma karfafa dunkulewar duniya. (Maryam)