in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta BRICS a Afirka ta Kudu
2018-06-13 10:24:46 cri
Ma'aikatar harkokin wasanni ta kasar Afirka ta Kudu ta sanar wa jakadan kasashe membobin kungiyar BRICS dake kasar Afirka ta Kudu a kwanakin baya cewa, kasar Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki ta kungiyar BRICS ta shekarar 2018 da za a yi a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu daga ranar 18 zuwa 22 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Za a shafe kwanaki 5 ana yin gasar ta wannan karo, za kuma a fafata ne a wasannin kwallon kafa mata na 'yan kasa da shekaru 17, kwallon raga na maza da mata 'yan kasa da shekaru 21, da kuma kwallon kwando salon Birtaniya mata na 'yan kasa da shekaru 19.

An gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta kungiyar BRICS ta shekarar 2017 a birnin Guangzhou na kasar Sin daga ranar 17 zuwa 21 ga watan Yuni na shekarar 2017, inda 'yan wasa kimanin 300 daga kasashen kungiyar BRICS suka halarci gasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China