David Makhura, ya bayyana haka ne yayin rufe taron kungiyar matasa ta diflomasiyya na kasashen BRICS a Johannesburg.
Ya ce Afrika ta kudu na farin cikin karbar bakuncin taron domin a cewarsa, zai ba 'yan kasuwa damar cudanya da takwarorinsu na kasashen BRICS, ya na mai cewa za su tabbatar da an gudanar da wasu taruka na daban, inda 'yan kasuwa za su samu abun koyo daga takwarorinsu na kasashen BRICS.
Ya kara da cewa, ya kamata nahiyar Afrika ta yi amfani da damar kasancewar Afrika ta kudu cikin kungiyar domin moriyarta, ya na mai cewa kasashen BRICS su ne jigo a fannin ci gaban fasahohi. (Fa'iza Mustapha)