Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wang Ping ne, ya shugabanci taron tattaunawar, shugaban majalisar harkokin lardunan kasar Afirka ta kudu Thandi Modise, da shugaban majalisar dattawan kasar Brazil Eunício Oliveira, da shugaban majalisar Duma ta kasar Rasha Vyacheslav Volodin, da mataimakin shugaba na farko na kwamitin tarayyar kasar Nikolay Fyodorov, da kuma shugaban majalisar dokokin kasar India Sumitra Mahajan sun halarci taron tattaunawar.
A yayin jawabinsa, Zhang Ping ya nuna cewa, kamata ya yi majalisun dokokin kasashen biyar su bi ra'ayin bai daya da aka cimma a yayin taron tattaunawar da aka shirya a birnin Xiamen na kasar Sin, don inganta yin kwaskwarima kan tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa, kana da kara yin cudanya kan fasahohin da suka samu wajen gudanar da harkokin kasa, ta yadda za a samar da wani muhallin doka da oda wajen hadin kan kasashen BRICS. (Bilkisu)