Mataimakiyar ministar harkokin wajen kasar Afrika ta kudu, Reginah Mhaule, ta bayyana hakan ne a lokacin da take gabatar da jawabi a wani taron karawa juna sani game da kungiyar BRICS a Afrika.
Mhaule tace, sun yarda cewa tasirin kungiyar a matakin kasa da kasa ya bada gudunmowa wajen kara bunkasa cigaban tattalin arziki da siyasar duniya. Kuma cigaban da aka cimma kawo yanzu ya samu ne sakamakon yin aiki cikin hadin gwiwa da kuma aiwatar da dukkannin yarjejeniyoyin da aka kulla wadanda a ko da yaushe ake kulla su bisa amincewar juna.
Tace kasar Afrika ta kudu ta shiga cikin BRICS ne domin kawo daidaito a harkokin kasa da kasa. Tace wadannan kasashen sun yi hadin gwiwa da juna ne bisa manufar kawo sauye sauye a tsarin duniya da nufin yin tasiri game da tsarin fada a ji a duniya, tattalin aziki, raya al'adun da kuma yanayin zamantakewar al'umma baki daya.
Kasar Afrika ta kudu ce zata karbi bakuncin taron kolin BRICS karo na 10 a wata mai zuwa.