Sahraoui ya bayyana cewa, halin rashin tabbas da ake fuskanta a duniya yanzu, ya kasance wata dama ga tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS, kuma kungiyar BRICS za ta zama wata kungiya mai farfado da tattalin arziki da kwanciyar hankali a fannin siyasa.
Sahraoui ya kara da cewa, tsarin samun bunkasuwa na kasar Sin ya jawo hankalin kasashen duniya da dama, domin ba shi da wata alamar mulkin mallaka, kana ba ya tilastawa sauran kasashen duniya amfani da ra'ayinta. (Zainab)