in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Rasha: tsarin kasashen BRICS na kara yin tasiri a duniya
2018-03-06 09:52:54 cri
Ministan harkokin wajen Rasha Sergej Lavrov, ya jadadda cewa, tsarin kasashen BRICS yana kara yin kyakkyawan tasiri a duniya, sa'an nan kasashen duniya suna kara sha'awar kasashen kungiyar.

Rahoton da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafinta na Internet a jiya Litinin ya ruwaito Ministan na bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labaru.

Sergej Lavrov ya kara da cewa, tarurruka a matakai daban daban da dandalin al'umma a fannoni daban daban karkashin tsarin kasashen BRICS, sun ja hankalin kafofin yada labaru da masana.

Ya ce, kudurorin masu ruwa da tsaki da kasashen BRICS suka tsai da, ba kasashen kungiyar 5 kadai suka shafa ba, inda ya ce, sun yi tasiri kan harkokin siyasa da tattalin arzikin duniya, lamarin da ya sa kaimi kan samar da tsari mai adalci a matakai daban daban a duniya. Tsarin kasashen na BRICS ya zama misali wajen inganta hulda da hadin gwiwa a tsakanin sassa daban daban cikin al'amuran kasa da kasa.

Ministan ya ce, kasar Afirka ta Kudu ita ce shugabar kungiyar kasashen BRICS a bana, kuma kasashen na BRICS za su mai da hankali kan manyan matsaloli da kalubale da ake fuskanta a nahiyar Afirka, kana sabon bankin raya kasashen BRICS zai samar da sabon zarafi wajen zurfafa tattaunawa da nahiyar Afirka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China