A yayin taro kan batun nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa da kwamitin sulhu na MDD ya kira a jiya, Wu Haitao, ya bayyana cewa, a halin yanzu, akwai kasashe da dama dake fama da matsalar fashewar nakiyoyi, kuma yake-yake da tashe-tashen hankali da suka faru a wasu yankuna sun haifar da karin matsalolin tashin boma-bomai ga al'ummomin da abin ya shafa. Kuma, a shekarun baya bayan nan, 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi sun ci gaba da yin amfani da boma-bomai masu saukin sarrafawa domin kai hare-hare.
A don haka ya ce, karfafa hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar warware matsalar nakiyoyi yana da muhimmiyar ma'ana wajen kiyaye tsaron al'ummomi da dukiyoyinsu, da tabbatar da gudanar aikin kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata da kuma cimman burin neman dauwamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030.
Bugu da kari, Mr. Wu ya ce, kasar Sin ta ba da taimako wajen kawar da nakiyoyin da aka binne, ga kasashen Asiya da Latin Amurka sama da 40 ta hanyar samar musu na'urorin kawar da nakiyoyin da aka binne da kuma horar da ma'aikatansu. (Maryam)