Da yake jawabi ga zauren majalisar, Antonio Guterres ya ce gazawa wajen samun ci gaba ta fuskar samar da kudin wanzar da zaman lafiya zai illata yukurin da suke na ceton rayuka da daidaita kasashen dake fama da rikici da rage wahalhalun jama'a da kuma kare masu rauni. Inda ya ce suna ganin yadda mutane ke wahala a wani irin yanayi mai sarkakiya.
Ya ce asunsun da aka kaddamar a 2006 domin tallafawa ayyuka da shirye shirye da hukumomin dake kokarin samar da dawwamammiyar zaman lafiya a kasashen dake fama da rikici, muhimmin abu ne wajen wanzar da zaman lafiya, yana mai cewa zai iya samun kudade daga wasu bangarori da samar da kudaden gudanar da ayyukan da wasu za su yi fargabar zuba musu jari.
Galibin shirye-shiryen asusun na mayar da hankali ne ga tallafawa mata da matasa. (Fa'iza Mustapha)