in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta amsa tambayoyin WTO
2018-06-28 20:09:00 cri
Yau Alhamis, ofishin watsa labarai na kasar Sin ya fidda takardar "Sin da WTO" karo na farko, inda ya yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta cika alkawarinta, da kuma bayar da gudummawa bayan ta shiga kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO a shekarar 2001.

Ko kasar Sin ta cika alkawarinta na shiga kungiyar?

Tun lokacin da Sin ta shiga kungiyar a shekarar 2001, ta dukufa wajen daidaita ka'idodi, da dokokin gwamnatin tsakiya da na gwamnatocin wuraren kasa, domin cika alkawarinta ta fuskar cinikin hajoji, da cinikin ba da hidima, da kuma kare ikon mallakar fasaha. Har ila yau adadin kudin kwastan da kasar Sin ta karba kan hajoji ya ragu daga 15.3% a shekarar 2001 zuwa 9.8% a shekarar 2010.

Yadda kasar Sin ta canja duniya bayan ta shiga WTO?

Tun shekarar 2002, ya zuwa yanzu, matsakaiciyar gudummawar da Sin ta bayar kan karuwar tattalin arzikin duniya ya kai kimanin 30%, lamarin da ya sa, Sin ta kasance muhimmin karfi na raya tattalin arzikin duniya.

Mene ne darussan da Sin ta koyarwa duniya?

Kara bude kofa ga waje da kasar Sin take aiwatarwa a halin yanzu, zai samar da damammaki masu kyau ga kasa da kasa wajen neman bunkasuwa. Muddin, kasashen duniya sun bi ka'idojin WTO, za a iya karfafa dunkulewar kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China