in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da takardar bayani game da kungiyar WTO karo na farko
2018-06-28 16:30:59 cri
Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da takardar bayani mai taken "Sin da kungiyar WTO" a yau Alhamis, wannan ne karo na farko da Sin ta gabatar da takardar a wannan batu.

Takardar ta ce, bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO a shekarar 2001, ta kyautata tsarin tattalin arzikinta na gurguzu, tare da daidaita ka'idojin cinikinta bisa ga ka'idojin ciki da ke tsakanin bangarori daban daban, ta kuma cika alkawarinta na bude kofarta ga kayayyaki da hidima da aka samar daga kasashen waje. Baya ga haka, ta kuma inganta aikin kare ikon mallakar ilmi, da inganta manufofin bude kofa ga kasashen waje, ta haka ta samar da gudummawa ga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban.

Bayan da ta shiga kungiyar WTO, Sin ta tsaya tsayin daka kan kiyaye tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, tare da shiga ayyukan hukumar a dukkan fannoni. Ta kuma sa kaimi ga kungiyar WTO da ta dora muhimmanci a kan bukatun kasashe masu tasowa da ke da wakilci a cikin kungiyar, da yaki da ra'ayin bangaranci da ra'ayin kariyar ciniki, da kuma kara sa kaimi ga kungiyar WTO da ta ba da gudummawarta ta fannin dunkulewar tattalin arzikin duniya na bai daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China