in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farar takarda: Kasar Sin ta cika ka'idojin WTO game da 'yancin mallakar fasaha
2018-06-28 17:03:07 cri
Wata farar takarda da ofisihin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar a yau Alhamis mai taken "Kasar Sin da hukumar cinikayya ta duniya" ya nuna cewa, kasar Sin ta cika dukkan ka'idojin da aka gindaya game da 'yancin mallakar fasaha.

Takardar ta ce, kare 'yancin malkakar fasaha shi ne kashin bayan inganta tsarin 'yancin mallakar fasaha, kana zai bunkasa takarar a tattalin arzikin kasar Sin. Haka kuma tsarin ba kawai zai taimakawa yadda kasar Sin za ta raya kanta kadai ba, har ma zai taimaka wajen samar da yanayin da ya dace na harkokin cinikayya kamar yadda doka ta tanada.

Tun lokacin da kasar Sin ta shiga hukumar WTO, kasar ta bullo tare da inganta dokoki da ka'idojinta game da kare 'yancin mallakar fasaha, kana ta hada kai da kasashe da dama kan yadda za a kare 'yancin mallakar fasaha, da martaba dokokin kasa da kasa, da bullo da wasu dokokin da abin ya shafa kamar yadda dokokin WTO suka tanada kana suka dace da halin musamman na kasar Sin.

Daga karshen takardar ta bayyana cewa, kasar Sin ta kafa kotunan kula da batutuwan da suka shafi kare 'yancin mallakar fasaha guda uku a garuruwan Beijing, da Shanghai da kuma Guangzhou da wasu sassan shari'a na musamman a matsakaitan kotuna na 15 a garuruwan Nanjing, da Suzhou, da Wuhan da Xi'an da kuma wasu biranen kasar da za su kula da batutuwan da suka shafi kare 'yancin mallakar fasaha da suka shafi yankunan kasar, ciki har da wadanda suka shafi tambarin mallaka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China