in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana: Bude kofar kasar Sin ya zarta alkawuran da ta dauka a WTO
2018-06-28 10:42:45 cri
Wasu masanan kasar Sin sun bayyana cewa a cikin wasu gwamman shekaru da suka gabata tsarin bude kofar kasar Sin ya zarce alkawuran da ta dauka lokacin shigarta kungiyar ciniki ta kasa da kasa wato (WTO). Song Hong, wani manazarci a cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin yace, kasar Sin ba wai kawai tana sauke nauyin dake wuyanta karkashin wakilcin kungiyar WTO ba ne, har ma tana kara bude kofarta. Tun bayan da ta zama mambar WTO a shekarar 2001, sannu a hankali kasar Sin ta kafa tsarin haraji da ya yi daidai da tsarin tattalin arzikinta na cikin gida da kuma na kasa da kasa, inji Tu Xinquan na jami'ar nazarin ciniki da tattalin arziki ta kasa da kasa. Kasar Sin ta riga ta cika alkawarinta na rage kudaden harajin hajojinta daga shekarar 2010, inda ta rage adadin harajin daga kashi 15.3 bisa 100 a shekarar 2001 zuwa kashi 9.8 bisa 100. Bude kofar kasar Sin zai kara samarwa duniya damammakin zuba jari, inji Niu Li, wani masanin tattalin arziki a cibiyar yada labarai mallakawar kasar Sin. A cewar Niu, nan da shekaru 5 masu zuwa, an yi hasashen kasar Sin zata shigo da hajoji daga waje na adadin dalar Amurka trillion 8 kana zai janyo hankalin masu zuba jari daga waje na kimanin dala biliyan 600.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China