in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar bayanai: Sin tana goyon bayan warware takaddamar ciniki karkashin dokokin WTO
2018-06-28 16:55:13 cri
Wata takardar bayanai da aka fitar a yau Alhamis ta nuna cewa kasar Sin tana bada muhimmanci ga yarjejeniyar kungiyar kasuwanci ta kasa da kasa WTO wajen yin amfani da ka'idojin kungiyar a matsayin hanyar warware duk wata takaddamar ciniki tsakanin kasashe mambobin kungiyar ta WTO.

A takardar bayanan, mai taken "Sin da WTO", wanda ofishin yada labaru na majajisar gudanarwar kasar Sin ya fitar, da nufin yin cikakken bayanai game da matsayin kasar Sin na sauke nauyin dake wuyanta game da tsarin na WTO.

Amfani da ka'idojin WTO wajen warware dukkan takaddama yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da yin hasashe game da tsarin cinikayya na kasa da kasa da dorewar tsarin kasuwanci tsakanin gamayyar kasashen duniya, in ji takardar bayanan.

A cewar takardar bayanan, kasar Sin tana goyon bayan mambobin kungiyar WTO da su warware takaddamar ciniki a tsakaninsu karkashin tsarin ka'idoji na kungiyar WTO.

Ya zuwa watan Afrilun shekarar 2018, kasar Sin ta gabatarwa WTO bukatun neman warware sabani kimanin 17, inda 8 daga cikinsu tuni an riga an kammala su. Haka zalika, kasar Sin ta gabatar da korafe-korafe kimanin 27, inda aka warware kimanin 23 daga cikinsu, kamar yadda takardar bayanan ta tabbatar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China