Takardar bayanan ta ce, Sin na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, na ganin ta bude kofarta ga dukkanin kasashe ta fuskar hada hadar cinikayya da harkokin zuba jari. Tana kuma kokarin ganin ta karfafa matakan warware sabani a duk lokacin da aka fuskanci hakan.
Kaza lika takardar ta bayyana kudurin Sin, na ci gaba da martaba ka'idojin kungiyar WTO, da sauran tsare tsaren gudanar da kasuwanci a bude, ba tare da nuna wata wariya ko banbanci ba.
Har wa yau takardar ta bayyana Sin a matsayin mai taka rawar gani, da habaka goyon bayan ci gaban hada hadar cinikayya tsakanin dukkanin kasashe da yankuna.
A daya bangaren kuma, Sin na ci gaba da bude kofar gudanar da kasuwanci maras shinge, da kuma fadada zuba jari, tare da mara baya ga tattaunawar Doha ta kyautata hada hadar cinikayya. (Saminu Hassan)