in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar bayanai: Sin na kara fadada manufofin ta na bude kofa
2018-06-28 17:06:59 cri
Wata takardar bayanai da ofishin watsa labarai na kasar Sin ya fitar a Alhamis din nan, ta ce Sin na ci gaba da fadada manufofinta na bude kofa ga kasashen waje.

Takardar ta ce, Sin na gudanar da hada hadar cinikayya da ke amfanar dukkanin sassa, ta yadda kowane bangare zai samu moriya, da fadadar ci gaba cikin daidaito.

Sin ba ta taba neman ribar da ta wuce iyaka da gangan ba, yayin da take mu'amalar cinikayya da sauran kasashe. Kana kasar har kullum tana maraba da shigar da hajojin sauran kasashe cikin kasuwanninta, da kara inganta musaya tsakanin al'ummu daban daban, tare da daga darajar masana'antu.

Takardar ta kara da cewa, Sin za ta ci gaba da inganta hada hadar kasuwanci tsakanin kasa da kasa, tare da kara fadada damar da masu zuba jari daga kasashen ketare ke da ita a sassan yankunan ta.

Har wa yau za ta samar da karin kyakkyawan yanayi ga masu sha'awar zuba jari, da kayyade tsare tsaren fidda jarin ta waje, tare da goyon bayan kafuwar tsare tsaren yankunan ciniki cikin 'yanci, kamar dai yadda takardar bayanan ta bayyana. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China