in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya gana da tawagar wakilan 'yan sandan Sin
2018-06-24 16:47:02 cri
A ranar 22 ga wata, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya gana da tawagar wakilan kasar Sin wadda ta halarci taron kolin shugabannin 'yan sanda na MDD karo na biyu da aka yi a birnin New York.

A yayin ganawar tasu, Mr. Guterres ya yabawa kasar Sin kan babbar gudummawar da ta bayar a aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. Ya ce, 'yan sandan kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta zaba suna da kwarewa, kuma suna bin ka'idodin ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD yadda ya kamata, lamarin da yasa suke samun yabo daga bangarori daban daban. Kuma MDD ta yabawa kasar Sin kan yadda take karfafa karfin 'yan sandanta wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, tana saran kasar Sin zata bada karin gudumamwa a wannan fanni.

Shugaban tawagar, kana zaunannen mataimakin ministan kula da tsaron jama'ar kasar Sin Wang Xiaohong ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da shugaban kasar Xi Jinping ya kulla tare da babban magatakardan MDD Antonio Guterres, za kuma ta cigaba da goyon bayan MDD kan ayyukan kiyaye zaman lafiya da kuma kara karfin 'yan sandan kiyaye zaman lafiyar, ta yadda Sin za ta bada karin gudummawa wajen kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da MDD wajen kare tsaron yankunan da shirin "Ziri daya da hanya daya" ya shafa, da hana yaduwar mugun kwayoyi, da yaki da ta'addanci da dai sauransu, domin kara tallafawa al'ummomin kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China