in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Dakile barkewar rikici ne hanya mafi dacewa ta ba da kariya ga fararen hula
2018-05-23 11:08:15 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce babu wata hanya mafi dacewa ta ba da kariya ga fararen hula, wadda ta wuce dakile barkewar rikici, ko kawo karshen su.

Mr. Guterres ya bayyana hakan ne a wani zama na kwamitin tsaron MDD, inda aka yi mahawara game da kariya ga fararen hula. Ya ce, kare barkewar rikici, da wanzar da sulhu, da samar da yanayin zaman lafiya, su ne kan gaba a matakan da MDD ke dauka a ko da yaushe.

Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, duk da yake ana tunkarar rashin tabbas yayin da yankuna da dama ke fuskantar kwararar 'yan gudun hijira, da fargabar karancin abinci, da keta hakkokin bil Adama sakamakon tashe tashen hankula, a hannu guda akwai fatan cimma nasarar da aka sanya gaba.

Daga nan sai ya yi kira ga mambobin majalissar, da su samar da tsare tsare na baiwa fararen hula kariya a yankunan da ake fama da rikici, tare da tabbatar da ana fitar da halin da ake ciki game da cin zarafin bil Adama a fili, ga sassan masu ruwa da tsaki.

Guterres ya kuma shaidawa kwamitin tsaron MDDr cewa, sama da mutane miliyan 128 a sassan duniya daban daban, na bukatar agajin jin kai, kuma mafi yawan wannan adadi sun fada cikin halin na matsi ne, sakamakon barkewar tashe tashen hankula.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China