in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kasa da kasa a Morocco kan ayyukan wanzar da zaman lafiya a Afrika
2018-06-19 11:01:59 cri
An bude taron kasa da kasa na yini 2 jiya Litinin a Rabat babban birnin Morocco, domin tattauna kalubalen dake tattare da ayyukan wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Taron wanda cibiyar bincike ta OCP Morocco ta shirya, ya samu halartar daruruwan jami'ai da suka hada da manyan jami'an soji da lauyoyi da shehunan malaman jami'o'i da kuma wakilan hukumomin kasa da kasa.

Da yake jawabi, tsohon ministan harkokin wajen Morocco Youssef Amrani, ya jadadda cewa, sarkakiya da ta'azarrar rikici a nahiyar, ya nuna cewa ayyukan wanzar da zaman lafiya da na soji kadai, ba za su iya zama ingantattun hanyoyin magance rashin tsaro da kaifin kishin addini a nahiyar ba.

Ajandar taron ta kunshi muhimman bangarorin ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban da sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD suka samu da aikin kare fararen hula yayin gudanar da ayyukan da horar da jami'an wanzar da zaman lafiya da kuma rawar da Tarayyar Afrika ke takawa cikin ayyukan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China