in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya yi alkawarin kyautata shirin wanzar da zaman lafiya
2018-05-25 10:01:32 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi alkawarin daukar matakan da suka dace wajen inganta tsaro a shirin wanzar da zaman lafiya.

Babban jami'in MDDr ya furta hakan ne a wani sakon da ya gabatar na murnar tunawa da zagayowar ranar shirin wanzar da zaman lafiyar ta MDD, wanda aka kebe ranar 29 ga watan Mayun kowace shekara, ya ce kasancewa wannan aiki ne da ake gudanar da shi na sadaukar da kai a duk fadin duniya, ya ce a shirye suke su dauki dukkan matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaro a shirin wanzar da zaman lafiya, da daukar matakan da za su tabbatar da ba da kariya ga rayukan jami'an shirin wanzar da zaman lafiyar, musamman a yankunan da ake fuskantar kalubaloli.

Ya kara da cewa, a shirye suke su kara jaddada muhimmiyar rawar da jami'ansu ke takawa wajen ci gaba da kare hakkin bil adama da kuma magance matsalolin da suka shafi cin zarafin da yin fyade ga fararen hula.

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1948, kwamitin sulhun MDD ya fara kaddamar da shirinsa na wanzar da zaman lafiya, aikin hukumar wanzar da zaman lafiyar MDDr ya fara ne a yankin Gabas ta Tsakiya.

Guterres ya ce, a wannan biki karo na 70, suna jinjinawa maza da mata sama da miliyan daya wadanda suka yi aiki karkashin tutar MDDr, sun ceto rayukan al'umma da ba za su lissafu ba.

Ya kara da cewa, suna karrama jami'an shirin MDD sama 3,700 wadanda suka sadaukar da rayuwarsu karkashin wannan shirin. Kuma suna jinjinawa rundunoni 14 a fadin duniya da suke aiki ba dare ba rana don kare rayukan al'umma da tabbatar da zaman lafiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China