in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shirya dandalin tsaron Sin da Afirka karo na farko a Sin
2018-05-31 19:20:11 cri

A yau Alhamis kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Ren Guoqiang, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, ma'aikatarsa za ta shirya dandali kan tsaron Sin da Afirka karo na farko a kasar Sin, tsakanin ranekun 26 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yuli, inda za a gayyaci shugabannin hukumomin tsaron kasashen Afirka, da manyan jami'an rundunonin sojojin kasashen, da shugabannin kungiyoyin shiyya shiyya domin halartar dandalin.

Babban taken dandalin shi ne "hadin gwiwa da taimakon juna", manyan batutuwan da za a tattauna a kai kuwa sun hada tsaron shiyya shiyya, da gina karfin samar da tsaro a kasashen Afirka bisa dogaron kansu, da hadin gwiwa kan tsaro tsakanin Sin da Afirka da sauransu. Wakilan hukumomin tsawon kasashen Afirka wadanda za su halarci dandalin za su samu damammakin ziyarar rundunonin sojojin kasar Sin na kasa, da ruwa, da kuma sama.

Ren Guoqiang yana mai cewa, yana cike da imani, dandalin zai zama wani muhimmin dandalin sa kaimi kan zaman lafiya da ci gaba, da hadin gwiwa ga sassan biyu wato Sin da Afirka, haka kuma zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a duk fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China