in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe dandalin kasa da kasa na yaki da ta'addanci a Beijing
2018-05-31 19:12:38 cri

A yau Alhamis ne aka rufe dandalin kasa da kasa na yini hudu mai taken "babbar ganuwa-shekarar 2018", wanda aka shirya a nan birnin Beijing domin yaki da ta'addanci. Wakilai mahalartar dandalin sama da 180 daga Sin, da Faransa, da Pakistan, da Jordan, da Masar, da Mexico da sauran kasashe 22, sun yi tattaunawa mai zurfa kan batun yaki da ta'addanci a tuddai.

Kwamandan rundumar 'yan sandan kasar Sin Wang Ning ya gabatar da wani jawabi a gun bikin rufe dandalin, inda ya bayyana cewa, makasudin shirya dandalin shi ne, samar da wani dandali ga kasa da kasa domin su yi musanyar bayanai, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin.

Mataimakin shugaban hukumar hulda da kasashen waje ta ma'aikatar tsaron Najeriya Adesope, shi ma ya gabatar da wani jawabi yayin taron, inda ya bayyana cewa, wadata da ci gaba suna dogaro ne kan zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya ce idan aka gaza dakile yaduwar ta'addanci, to ba zai yiwu a tabbatar da zaman lafiya ba. Ya ce ana bukatar irin wannan dandali mai lakabin "babbar ganuwa", domin kara karfin tunkarar ta'addanci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China