Da yake ganawa da Xinhua, Jakadan ya ce zaman lafiya da tsaro babban bangare ne da kasar Sin da AU da kuma kasashen Afrika ke hadin gwiwa, inda kasar Sin ke taimakawa da dakaru da kuma shirye shiryen horo.
Jami'in na magana ne a karshen taron manyan jami'ai da aka yi kan tsaro a nahiyar a Afrika, wanda ya gudana a birnin Bahir Dar na arewacin Habasha daga ranar 21 zuwa 22 ga watan nan.
Kuang Weilin ya ce a yanzu, kasar Sin na aiki kafada da kafada da AU, domin cika alkawarin nan na 2015, dake da nufin samar da tallafin dala miliyan 100 ga Rundunar ko-ta-kwana ta Afrika wato ASF.
Ya ce idan babu zaman lafiya da tsaro, to ba za a samu ci gaba ba, a don haka, za su yi duk abun da za su iya wajen bada gudunmuwa ga zaman lafiya da tsaro a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)