in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayin diflomasiyyar Xi Jinping shi ne manufar diflomasiyya da Sin za ta bi cikin sabon zamani
2018-06-24 16:30:04 cri
Yau Lahadi, jaridar People's daily ta fidda sharhi cewa, ra'ayin diflomasiyyar Xi Jinping shi ne manufar diflomasiyyar da kasar Sin zata bi cikin sabon zamani.

Cikin sharhin jaridar an bayyana cewa, a shekaru 5 da suka gabata, an cimma sakamako masu yawa a fannin diflomasiyya bisa jagorancin kwamitin tsakiyar JKS dake karkashin jagorancin Xi Jinping, da kuma jagorancin kimiyya da fasaha da manufar diflomasiyya ta tsarin gurguzu cikin sabon zamani, wato ra'ayin diflomasiyyar Xi Jinping ya dace.

Inganta aikin diflomasiyya domin cimma burin farfadowar kasar Sin, da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummar kasa baki daya shi ne burin da aka sanya gaba ta fuskar harkokin diflomasiyya. Ya kamata a ci gaba da aiwatar da manufofin diflomasiyya bisa tushe, da mayar da hankali kan al'ummomin kasar da samar da yanayi da damammaki masu kyau ga bunkasuwar kasar Sin.

Kuma, wajibi ne a bi hanyar zaman lafiya wajen neman bunkasuwa, da kuma bisa tushen girmama juna da cimma moriyar juna. wannan shi ne kudurin da aka tsaida bisa halin da kasarmu take ciki da kuma bukatunmu. Ana bukatar girmama juna domin kiyaye zaman lafiya, kana, ana bukatar yin hadin gwiwa domin neman ci gaba tare. Ya kamata dukkan kasashen duniya su bi hanyar zaman lafiya a yayin da suke neman bunkasuwar kansu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China