Sin dai na fatan hakan zai ba da wata kafa, ta cimma nasarar kawo karshen makaman nukiliya a zirin Koriya, tare da wanzar da zaman lafiya da lumana a zirin.
Wata kafar watsa labaran Koriya ta arewa (DPRK) ta bayyana a Larabar nan cewa, Pyongyang ta dage aniyar tattaunawar manyan jami'ai tare da Koriya ta kudu, kana mai yiyuwa ne za ta janye daga tattaunawar da aka tsara gudanarwa da tsagin Amurka, sakamakon atisayen soji na hadin gwiwa da Amurka ke gudanarwa tare da Koriya ta kudu a halin yanzu. (Saminu Hassan)