Kimanin akwatunan abinci 250 aka rarraba, kana mutane sama da 400 ne suka halarci bude bakin, a lokacin da al'ummar Musulmi ke bude bakin azumin watan Ramadan.
Ana sa ran raba akwatunan abinci kimanin 2,000, kana mutanen 5,000 ne ake fatan za su amfana da abincin bude bakin, wanda kamfanonin kasar Sin za su raba nan da kwanaki 15 masu zuwa a fadin kasar ta Masar, wanda ya hada da lardunan Cairo, Giza, Fayoum, Beni Suef da Aswan.
An shirya bada tallafin ne bisa hadin gwiwar ofishin jakadancin kasar Sin dake Masar da kuma majalisar kula da harkokin ciniki da masana'antu ta kasar Sin dake Masar, tare da hadin gwiwar kungiyar raya cigaban Masar. (Ahmad Fagam)