in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan kasar Sin ya bukaci a kara tuntubar juna tsakanin Sin da Amurka don kaucewa rashin fahimta
2018-06-09 16:42:06 cri
Jakadan kasar Sin a Amurka Cui Tiankai, ya ce kasashen Sin da Amurka za su karfafa tuntubar juna da hadin gwiwa domin kaucewa rashin fahimtar juna.

Jakadan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka John J. Sullivan a jiya, inda suka yi musayar ra'ayi kan dangantakar dake tsakanin kasashensu, da sauran batutuwan da suka shafe su.

Cui Tiankai, ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka na cikin wani muhimmin lokaci, kuma bangarorin biyu za su karfafa tuntubar juna da hadin gwiwa da kara aminta da juna da kuma kula da sabanin da ke tsakaninsu domin kaucewa rashin fahimta.

Ya kuma jadadda cewa, kasashen biyu na da nauyin da ya rataya a wuyansu, na tabbatar da karewa da tsaron halatattun hakoki da manufofinsu na diflomasiyya da kuma wakilansu dake kasashensu. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China