Ministar harkokin wajen kasar Ghana za ta kawo ziyara Sin
2018-06-08 19:09:55
cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Jumma'a cewa, ministar harkokin wajen kasar Ghana Shirley Ayorkor Botchwey za ta kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 10 zuwa 15 ga watan Yuni da muke ciki, bisa gayyatar takwaranta kana mamba a majalisar gudanarwar kasar ta Sin Wang Yi. (Ibrahim)