in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da Sidiki Kaba
2018-06-21 10:01:55 cri
Mambar ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mista Yang Jiechi, ya gana da ministan harkokin waje na kasar Senegal Sidiki Kaba a jiya 20 ga wata a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya nuna cewa, a shekarun baya baya nan, karkashin jagorancin shugabanni Xi Jinping da Macky Sall, kasashen biyu sun daga matsayin dangantakar aboka dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare zuwa ga wani sabon matsayi. Sin na fatan kara hadin kai da Senegal don kara amincewa da juna ta fuskar siyasa, da kara tuntubar shugabannin biyu, da kara hadin kai cikin tsarin dandalin hadin gwiwar kasashen Sin da Afrika da MDD, ta yadda za a ciyar da dangantakar kasashen biyu gaba, da sa kaimi ga kafa kunigyar bai daya tsakanin Sin da Afrika.

A nasa bangaren, Kaba ya ce, Senegal da Sin na da dankon zumunci mai karfi tsakaninsu, kasar tana nacewa ga manufar kasar Sin daya tak a duniya. Shugaba Sall yana sa ran halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da za a gudanar a watan Satumba a birnin Beijing, kuma yana fatan zurfafa hadin kai tsakaninsu da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China