in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kuduri niyyar yin hadin gwiwa domin kara kula da yankin saman duniyar bil adama
2018-06-20 11:06:26 cri
Wakilin kasar Sin a MMD a Vienna, Shi Zhongjun, ya ce kasar Sin ta kuduri niyyar yin hadin gwiwa domin samar da ci gaba na bai daya ga yankin saman duniyar bil'adama, wanda ke zaman wani sabon dandali na inganta rayuwar dan adam.

Shi Zhongjun, ya ce bayan shafe sama da shekaru 60 ta na aiki tukuru, kasar Sin ta kafa nagartaccen tsarin kimiyyar sararin samaniya wanda ya zama muhimmin jigo wajen ganowa da amfani da yankin saman duniyar bil'adama.

Ya ce kasar Sin ta kuduri niyyar yin hadin gwiwa da kasashe domin kara kulawa da samar da ci gaban yankin, da nufin cin gajiyarsa da sauran kasashen.

A watan da ya gabata ne kasar Sin ta sanar da samar da wata na'ura dake shawagi a sama domin hadin gwiwa da kasashe mambobin MDD

Jami'in na kasar Sin ya yi wannan tsokaci ne a ranar da ake cika shekaru 50 da gudanar da taron MDD na farko kan yankin saman duniyar bil'adama. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China