in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU za ta kara haraji kan wasu hajojin Amurka daga ranar 22 ga wata
2018-06-21 09:52:00 cri
Kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai EU, ya fidda wata sanarwa a jiya Laraba cewa, kungiyar EU za ta kara kudin kwastan kan hajoji masu darajar Euro biliyan 2.8, wadanda za a shigo daga kasar Amurka tun daga ranar 22 ga watan Yuni, domin mai da martani kan Amurka dangane da karin kudin kwastan da ta karba kan kayayyakin ingantaccen bakin karfe da na samholo.

Kwamitin ya ce, hajojin da za a kara kudin kwastan a wannan karo sun hada da kayayyakin ingantaccen bakin karfe da samholo na kasar Amurka da kuma amfanin gona na kasar da dai sauransu, kuma matakin da kungiyar EU ta dauka ya dace da ka'idar kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO.

Wakilin ciniki na kungiyar EU Cecilia Malmstrom ya bayyana cewa, kudurin maras adalci da kasar Amurka ta tsai da ya sa kungiyar EU ta dauki wannan mataki.

A ranar 31 ga watan Mayun da ya gabata ne, ministan harkokin kasuwancin kasar Amurka Wilbur Ross ya sanar da cewa, tun daga ranar 1 ga watan Yuni, kasar Amurka za ta kara kudin kwastan na kashi 25 bisa dari kan kayayyakin ingantaccen bakin karfe da ta shigo da su daga kungiyar EU, kasar Canada da kasar Mexico, yayin da za'a kara kudin kwastan na kashi 10 bisa dari kan kayayyakin samholo na kasashen uku.

Bisa kididdigar da kungiyar EU ta yi, an ce, matakin da kasar Amurkar ta dauka ya haifar da tasiri kan hajoji masu darajar Euro biliyan 6.4, wadanda kungiyar EU za ta fitar da su zuwa ketare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China