in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar dabara ta EU domin kin sayar da kayayyaki da yawa cikin farashi mai rahusa ta saba wa ka'idar WTO, in ji wasu mambobin WTO
2018-04-27 15:49:57 cri
Kwamitin dake adawa da sayar da kayayyaki da yawa cikin farashi mai rahusa na kungiyar cinikayya ta kasa da kasa wato WTO, ya kira taro a birnin Geneva a ranar 26 ga wata, inda mambobin kungiyar da dama da suka hada da Saudiya, Sin, Rasha da dai sauransu, suka nuna damuwarsu kan sabuwar dabarar da kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU ta gabatar, domin kin sayar da kayayyaki da yawa cikin farashi mai rahusa. Sabo da suna ganin cewa, sabuwar dabarar ta saba wa ka'idar WTO.

Bisa sabuwar dabarar da kungiyar EU ta fidda, an ce, idan wata kasa ta gamu da matsalar rashin daidaito a kasuwanninta, kungiyar EU za ta yi amfani da farashin kasa da kasa wajen lissafin kudin da ta kashe yayin fitar da kayayyaki, a maimakon yin amfani da farashin kasar ita kanta, a yayin da take yi wa kasar bincike kan ko ta sayar da kayayyaki da yawa cikin farashi mai rahusa, ko a'a. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China