Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana yau Laraba a nan Beijing cewa, rahotannin da kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta fitar kan yankunan musamman na Hong Kong da Macao na kasar Sin, ba su yiwa Sinawa dadi ba ko kadan.
A jiya ne dai, kungiyar EU ta fitar da rahotaninta na shekara-shekara kan yankunan musamman na Hong Kong da Macao na kasar Sin, inda ta tsoma baki cikin harkokin yankunan 2. (Tasallah Yuan)