Rosario ya ce, "Muna kira ga bangarorin da abin ya shafa da su tabbatar da ganin an mutunta dokokin hukumar WTO a bangaren hada hadar ciniki na kasa da kasa. Za mu nazarci irin matakan da aka dauka ko sun dace da manufofin hukumar WTO", jami'in ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua suka yi masa kan wannan batu.
A cewar kakakin, EU ta lura da cewa matakin da Amurka ta dauka mai lamba 301 ya sabawa moriyar kasar Sin, kuma suna ci gaba da binciken da suke yi a kan batun tun a watan Augastan shekarar 2017. (Ahmad Fagam)