in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin hadin gwiwa na AU da EU da MDD ya lashi takobin inganta hadin gwiwa wajen yaki da safarar bil adama
2017-12-20 12:18:46 cri

Hadadden kwamitin da ta kunshi Tarayyar Afrika AU da Tarayyar Turai EU da kuma MDD kan batutuwan da suka shafi kaurar jama'a, ya lashi takobin karfafa hadin gwiwa domin datse hanyoyin safarar bil Adama da aikata muggan laifuka.

Wata sanarwa da AU ta fita jiya Talata, ta ce hadadden kwamitin ya kuma tattauna hanyoyin magance yanayin 'yan ci rani a kasar Libya.

Nauyin dake wuyan kwamitin shi ne, aiki da hukumomin Libya da nufin datse hanyoyin safarar bil Adama da aikata muggan laifuka, tare kuma da taimakawa kasashen 'yan ci rani na asali da wadanda suke yada zango, magance matsalar tun daga tushe ta hanyar samar da damarmakin samun ci gaba da kwanciyar hankali.

Kwamitin zai kuma yi aiki da hukumomin Libya wajen tabbatar da hukumomin kasashen waje da kungiyoyi masu zaman kansu, sun samu damar isa cibiyoyin da ake tsare 'yan ci rani ba tare da wani tarnaki ba, sannan su ba hukumomin damar yi wa 'yan ci rani da 'yan gudun hijira dake cibiyoyin da aka tsare su cikakkiyar rajista mai adalci.

Domin karfafa aikin kama masu safarar mutane da masu fasa kauri, AU, EU da MDD sun amince da samar da cibiyoyi a biranen Addis Ababa da New York da Geneva, domin inganta kokarin nahiyar Afrika da ta Turai da sauran bangarorin kasashen waje dake da nufin datse hanyoyin safara tare da hukunta masu laifi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China