in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU za ta kara taimakawa yankin Sahel ta fuskar tsaro
2018-02-24 12:59:51 cri

Tarayyar Turai wato EU ta ce za ta kara ba kasashe 5 na yankin Sahel da ke nahiyar Afirka taimako ta fuskar tsaro, a kokarin kyautata karfinsu ta fuskar tsaro da yaki da 'yan ta'adda.

Tarayyar EU da MDD da Tarayyar Afirka wato AU da kasashe 5 na yankin Sahel sun gudanar da taron manyan jami'ai jiya Jumma'a a birnin Brussels na kasar Belguim, inda sassa daban daban suka tsai da kudurin samar da tallafin kudi na Euro miliyan 414 wajen goyon bayan bunkasa hadaddiyar rundunar tsaro ta kasashe 5 na yankin Sahel da ma yankin baki daya.

Bisa tanade-tanaden da ke cikin sanarwar da EU ta fitar, za ta ba hadaddiyar rundunar tsaro ta kasashe 5 na yankin Sahel tallafin kudin Euro miliyan 100. Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar EU ta fi ba yankin Sahel tallafi, inda za ta ba da tallafin Euro biliyan 8 wajen raya yankin daga shekarar 2014 zuwa 2020. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China