in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU ta yi hasashen samun cigaban tattalin arziki a 2018 da 2019
2018-02-08 11:09:35 cri
A wani hasashen tattalin arziki na baya bayan nan da kungiyar tarayyar Turai (EU) ta gudanar, ta gano cewa, tattalin arzikin kasashen dake amfani da kudaden bai daya na euro da na kasashen EU zai cigaba da bunkasa a shekarun 2018 da 2019.

EU ta yi hasashen samun karuwar kashi 2.3 bisa 100 da kashi 2.0 bisa 100 a 2018 da kuma 2019, ga dukkan kasashen masu amfani da kudin euro da kasashen dake karkashin kungiyar EU.

Da ma dai EU ta yi hasashen samun karuwar tattalin arzikin da kashi 2.4 cikin 100 a kasashen masu amfani da kudin euro da mambobin EU a shekarar 2017, lamarin da ya zarta hasashen da aka yi, a sakamakon komadar tattalin arzikin da suka samu.

Pierre Moscovici, jami'i mai kula da sha'anin tattalin arziki da al'amurran kudi na EU ya bayyana cewa, wannan shine murmurewa daga komadar tattalin arziki mafi sauri da kasashen na EU suka samu a cikin shekaru 10, kana ya bukaci a cigaba da daukar matakan da suka dace don karfafa gwiwar kungiyoyin tattalin arziki da na hada hadar kudade, inda ya jaddada cewa kofofin samun damammakin yin sauye sauye a tsarin tattalin arziki ba lallai ne su kasance na har abada ba. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China